Wednesday, 13 December 2017

"Abin naki ya fara yin yawa">> Da alama akwai matsala a wannan hoton na Maryam Yahaya

 Maryam Yahaya sabuwar jarumar fina-finan Hausace me tasowa, tun bayan da ta fito a shirin fim din Mansoor, sai tauraruwarta ta fara haskakawa, masoyanta suka karu a kafofin sada zumunta na yanar gizo da kuma zahiri haka kuma taci gaba da fitowa a sabbin fina-finai dake daukar hankulan mutane.
Maryam din takan saka hotunanta da ta sha kwalliya kala-kala a a dandalinta na yanar gizo, kuma mutane, masoyanta suna yabawa, to saidai wannan karin an samu akasin haka.

Domin kuwa wancan hoton na sama da Maryam din ta saka da alama bai birge da dama daga cikin masoyan nata ba, duk kuwa da cewa wasu sun yaba, amma wasu da dama sun kushe wannan hoto na Maryam.

Karanta abinda mutane ke cewa akan wannan hoto:No comments:

Post a Comment