Saturday, 9 December 2017

Adam A. Zango zai shiryawa masoyanshi dake jihohin Arewa liyafar cin abinci daya bayan daya

Tauraron finafinan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya fitar da sanarwar cewa, zai bi duk jihohin Arewa guda goma sha tara ya shiryawa masoyanshi liyafar cin abincin dare saboda ya nuna godiya bisa soyayyar da suke mishi, Adamun zai shirya irin wannan liyafa ta farko a jihar Kano kuma dalilin hakane, kamar yanda yace, wasu masoyanshi dake sauran jihohi suka nuna damuwa.Hakan yasa ya fitar da sanarwar cewa ba a garin Kanon kadai zai shirya irin wannan liyafa ba, hadda duk sauran jihohin Arewacin Najeriya gaba daya.

A sati kusan biyu da suka gabatane, Adamun yaje kasar Kamaru inda mutane kimanin dubu goma suka taru dan kallonshi, idandai wannan ya tabbata to Adamun ne na farko a cikin masana'antar fina-finai ta Hausa da aka tabawa irin wannan taro

No comments:

Post a Comment