Tuesday, 19 December 2017

"Akan annabi babu abinda bazan iya yiba">>Ummi Zeezee ta bayyyana irin kirarin da babanta yake mata

Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta bayyana irin kirarin da marigayi, mahaifinta yake mata lokacin yana raye, Ummi tace babanta yana kiranta da sunan ta Annabi, saboda akan annabi(S.A.W), babu abinda bazata iya yiba, kamar yanda ta bayyana.
Gadai abinda Ummi din ta bayyana kamar haka:

"kaga 'yar Ibrahim(Jalo) ta Annabi, bahaguwa ba'a gane inda kika dosa sai mutum mai fahimtar gaske! Wannan shine kirarin da babana yakemin kenan kullum innaje gaidashi. Babana yana kirana da ta annabi dan yasan akan son annabi wallahi ba abunda bazan iyayiba. Ina kewarka baba. Allah ya jikanka.
Allah ya jikan dukkan musulmin da suka rigamu gidan gaskiya.

No comments:

Post a Comment