Sunday, 10 December 2017

Amarya Maryam Indimi da, mahaifinta, angonta da kawayenta

Amarya, Maryam Indimi kenan cikin kyakkyawar rigarta ta amarci, aanyi kasaitaccen shagali irin na gani na fada, kamar yanda mukai ta ganin hotunan yanda abubuwa suke gudana, koda ba'a fadaba, biki irin wannan, na masu hannu da shuni, kowa zaiyi tsammanin za ai abubuwan birgewa da ban sha'awa.



A wannan hoton na kasa, Amarya ce da kawayenta, inda suka sa kaya iri daya.
Wannan hoton kuwa na kasa Amaryarce da mahaifinta, Muhammad Indimi.
A wanan hoton na kasa kuwa, angone, Mustafa, yake cashewa a gurin shagalin bikin.
A wannan hoton kuwa, Amaryace tare da mahaifinta, a duk cikin hidimar aure babu inda keda taba zuciya da sa shauki, irin lokacin da za'a fitar da amarya daga gidansu zuwa gidan aurenta, a lokacinne zatayi bankwana da iyaye da 'yan uwa, da dama sai an zubar da kwalla a irin wannan guri.

No comments:

Post a Comment