Thursday, 14 December 2017

An tantance dandalin Adam A. Zango na shafin Instagram

Shafin sada zumunta da muhawara musamman ta hanyar wallafa hotuna, Instagram, ya tantance dandalin tauraron fina-finan Hausa, Adam A. Zango dake shafin, adamu dai yana da masoya da suke bibiuarshi a dandalin da yawansu yakai dubu dari biyar da daya, a lokcin yin wannan rubutu.A sati biyu da suka gabatane Adamun yaje kasar Kamaru inda masoyanshi kimanin su dubu goma suka fito dan kallonshi a gurin da yayi wasa. Zuwa yanzu jarumai maza na fina-finan Hausa biyu ne kawai aka tantance dandalinsu na shafin Instagram din, daga Ali Nuhu sai Adam A. Zango.


Muna taya Adamu Murna.

No comments:

Post a Comment