Friday, 15 December 2017

An yankewa sojan daya kashe farar hula biyar hukuncin kisa: Wani kuma daya kashe yaro ta hanyar gwale-gwale an yankemai hukuncin daurin rai-da-rai

Kotun soji dake Maiduguri, ta yankewa wani Soja me suna John Godwin hukuncin kisa bayan da aka sameshi da laifin kashe fararen hula biyar da aka ceto daga hannun kungiyar Boko Haram.Hukumar Sojin ta bayyana cewa an ceto fararen hular ana bincike akansu sai kawai John ya kashesu su biyar reras.

Haka kuma an yankewa wani sojan shima me suna Innocent Ototo hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan da kotun sojin ta sameshi da laifin kashe wani karamin yaro dan shekaru 13 da ya zaraga da cewa wai ya sacemai waya. Innocent yayi ta baiwa yaron gwale-gwale har wahala tasa ya mutu.

Haka kuma akwai wasu sojojin da suma su bitu da aka yankewa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 kowannensu bayan da aka samesu da laifukan mallakar harsai ba akan ka'idaba

No comments:

Post a Comment