Saturday, 2 December 2017

Anya korar da akawa Rahama Sadau tana aiki kuwa?: Kalli hotunan wani sabon fim din hausa data fito a ciki

Da alama korar da kugiyar MOPPAN ta yiwa tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau bata aiki a kanta, domin kuwa bayan shirya fim din Rariya da jarumar tayi a wannan shekarar wanda ya samu karbuwa sosai, har kuma ya amshi kyautar City People Award na fim din Hausa da yafi yin fice na wannan shekerar, ga kuma wani fim me suna "Dan Iya" wanda Rahama Sadau din da Sadik Sani Sadik suka fito a ciki.

Rahama Sadau na daya daga cikin mashirya shirin kuma ta fito jaruma a ciki.

Rahamar dai ta mika takardar neman afuwa akan abinda ta aikata ga kungiyar MOPPAN, amma har yanzu shiru, kuma ga dukkanin alama, koda wannan kora da aka yiwa Rahamar na shafar ayyukan ta, to ba sosai bane.
Daga irin hotunan da suka bayyana na wannan fim din, za'a iya hasashen cewa zai kunshi barkwanci da soyayya da kuma al'adun gargajiya irin na Hausawa.


No comments:

Post a Comment