Saturday, 16 December 2017

Anyi hawan Daba dan murnar cikar jihar Kaduna shekaru 100 da kafuwa

A yaune sarakunan gargajiya na Arewa suka hadu a garin Kaduna inda akayi hawan daba dan murnar cikar jihar ta Kaduna shekaru dari da kafuwa, sarakuna da fadawansu sun nuna kawa ta hanyar hawan dokunan da aka caba musu ado.


Jama'a da dama sun taru a dandalin murtala dake garin na Kaduna inda a nanne akayi wannan hawan Daba kuma abin ya kayatar sosai.
 An dai kafa jihar ta Kaduna wadda itace cibiyar Arewa, tun shekarar 1917 lokacin turawan mulkin mallaka.

No comments:

Post a Comment