Tuesday, 12 December 2017

Anyi kiran ayi fim dan fadakar da matasa masu nunawa junansu tsiraici da sunan soyayya

Fitacciyar korarriyar tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau ta saka wani sako da aka turamata inda me sakon yake rokon masu shirya fim suyi shirin fim akan dabi'ar wasu matasa dake wata kalar bakar soyayya.Sakon yace ya kamata ayi fim don jawo hankulan samari da 'yan mata akan bakar dabi'ar nunawa junansu tsiraici da sunan soyayya, yanda zakaga saurayi da nunawa budurwarshi tsiraicinshi shima ya bukaci ta nuna mishi nata.

Sakon yace abin yayi yawa tsakanin matasa kuma masu yin hakan suna ganin wayewane,  shiyasa yake kiran Rahamar dasu yi fim dan nuna illar yin hakan.
Allah shi kyauta, ya kuma shiryemu baki daya.

No comments:

Post a Comment