Sunday, 10 December 2017

Anyi shirin fim akan Maryam Sanda: Matar da ta kashe mijinta

Kannywood sun yi fim din Maryam Sanda da Bilyaminu marigayi
Fastar fim din ta nuna wata mata da jajayen kaya ta caka wa wani saurayi wuka lokacin yayi sujjada a sallah. Wasu na ganin yin fim din bai dace ba, musamman ganin yadda batun ke gaban kotu. Wasu kuma na ganin ma tunda wani ya rasu, bai kamata wasu su ci kudi da hakan ta hanyar fim ba.

Fim din ta kashe shi, fim ne da Jamilu Ahmad Yakasai ya shirya, kuma har sun fara sayar dashi a kasuwa. A labarin dai, kamar yadda aka ji a gaske, wata mata ce, ake zargin  tsananin kishi ya sanya ta kashe mijinta yana cikin sallah, saboda zai karo mata kishiya. 

Saidai masu yin fim din kamar ko da yaushe sukan fadi cewa suna fadakarwane ga al'umma.

A waje daya kuma, wasu na gani tunda batun yana kotu, bai kamata ayi fim din ba, ko ma kuma cewa wani ya rasa ransa a gaske, bai kamata ayi ffim a ci riba dashi ba.

naija.ng


No comments:

Post a Comment