Saturday, 2 December 2017

Ashe dai da sauranshi: Kalli ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung na ninkaya

Ministan matasa da wasanni kenan Solomon Dalung yana ninkaya a cikin wani kududdufi dake filin kwallon kafa na kasa dake Abuja, ya bayyana cewa ninkaya na daya daga cikin abubuwan da yake sonyi kuma tana taimakawa wajan kara lafiyar jiki.

Ashe dai da sauranshi?, lura da cewa mafi yawancin masu rike da mukaman gwamnati sun riga sun tara kiba, basa iya motsa jikinsu sosai, wasu kuma tsufa babu karfin motsa jikin, abin birgewane aga, musamman ministan matasa na motsa jiki haka.


No comments:

Post a Comment