Thursday, 28 December 2017

"Ba'a fitar da Yusu Buhari kasar waje ba">>Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasar Najeriya ta hannun me magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ta karyata rahoton da The Cable suka wallafa cewa an fitar da dan shugaban kasar, Yusuf Buhari zuwa kasar Jamus dan cigaba da duba lafiyarshi acan.Jaridar Daily Trust tace Garba Shehun ya aikawa wakilinta da sakon waya cewa maganar fitar da Yusuf Buhari kasar waje karyace, haka bbchausa ma ta rahoto cewa Garba Shehun ya gayamusu cewa ba'a fitar da Yusuf waje ba.

Amma da bbchausan suka tambayeshi shin akwai yiyuwar za'a fitar dashi kasar waje, sai Garban yace, danginshine kawai zasu iya fadar hakan.

No comments:

Post a Comment