Friday, 8 December 2017

"Bacci da aiki: Ganduje mai shayi ba sa'an babanka bane: Saida aka rage yawan ayyukan da shugaba Buhari zai kaddamara Kano saboda yawansu"

Ayyukan da gwamnatin jihar Kano tayi wadanda aka tsara shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar dasu, sun kai guda goma sha hudu, dalilin haka yasa fadar shugaban kasa ta rage yawansu, ba duka shugaba Buharin ya kaddamar dasu ba.Me kula da shafukan yanar gizo na gwamnatin jihar, Salisu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka a wani sakon daya fitar ta dandain Twitter, ga abinda ya rubuta kamar haka:

"Saboda yawan ayyukan da aka tsara shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar a jihar Kano(guda goma sha hudu), wanda gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi, saida fadar shugaban kasa ta rage su, bacci da aiki, Ganduje mai shayi ba sa'an babanka bane"

Ansha dai yiwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje tsiya da cewa ya cika yin bacci sannan kuma wani tallafin da ya baiwa masu tsayi a jihar Kano shima ya jawo cece-kuce

No comments:

Post a Comment