Thursday, 21 December 2017

"Ban iya turanciba: Masu damuna akan turanci ku shafamin lafiya">>Adam A. Zango

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango ya bayyana cewa bai iya turanciba a cikin wannan bidiyon, Adamun yace masu damunshi da cewa bai iya turanci ba kokuma suna gwada  basirarshi da irin jin turancin da yake su shafamai laifiya, dan wanda akeji yanayima yanzu a titi ya koyeshi.Adamun ya kara da cewa da hausa yake fim yake waka dan haka baiga dalilin da zaisa ata damunshi da bayajin turancin ba.

Domin jin ainihin abinda Adamun yake fada sai a kalli wannan bidiyon na sama.

No comments:

Post a Comment