Friday, 1 December 2017

Beraye, kyankyasai da kuma kwari sun mamaye fadar shugaban kasar Amurka

The White House, 1800, Washington DC, District of Columbia.
Ma'aikata a fadar shugaban kasar Amurka ta White House, sun koka da mamayar da beraye, kyankyasai da kuma kwari sukawa ofisoshinsu, wannan ya bayyanane a cikin wata takardar gyare-gyare da aka yiwa fadar.

Kafar watsa labarai ta NBC ce ta bayyana cewa ta samu takardun gyaran da akawa fadar shekaru biyu da suka gabata, inda aka bukaci bangarorin ma'aikata daban-daban su mika irin gyare-gyren da dakuna da ofisoshinsu ke bukata.

A cikin takardun da aka mika na bukatar gyaran akwai wanda ofishin shugaban ma'aikata na fadar ya mika inda yayi korafin cewa ofishin nashi kwari sun addabeshi saboda haka yana bukatar gyara.

A shekarun bayane rahotanni suka bayyana cewa beraye sun hana shugaban kasa Muhammadu Buhari shiga Ofishinshi bayan ya dawo daga jiyyar rashin lafiya a kasar Ingila.

No comments:

Post a Comment