Tuesday, 5 December 2017

"Biliyan talatin gareni a asusun ajiyata na banki">>inji MC Tagwaye

Tauraron me wasan barkwancinnan ta hanyar kwaikwayon muryar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da ake kira da MCTgwaye, ya bayar da damar masoyanshi su tambayeshi duk wani abu da suke son sani game dashi, ta dandalinshi na sada zumunta da Muhawara, inda yace zai bayar da amsa.

Tambayoyi kala-kala sunyi ta fitowa daga gurin mutane, bayan da suka samu wannan dama:

Kamar dai yanda aka sanshi da bayar da dariya, wasu tambayoyin haka ya amsasu cikin raha.

Ga wasu daga cikin tambayoyin da aka mishi da kuma amsoshin daya bayar:
Wani ya tambayeshi, wai nawane a cikin asusun ajiyarshi na banki?

MC tagwaye ya bashi amsa da cewa, Biliyan talatinne.Wani ya tambayeshi, wai wayake ganin cewa zai lashe zabe?
Sai ya bashi amsa da cewa, wanda yafi yawan kuri'u.
Wani kuma ya tambayeshi, wai me zai hana ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2019 me zuwa? saboda ana bukatar matasa irinsu, mun gaji da wadannan tsofaffin mutanen.

Sai ya bashi amsa da cewa. bana son in mutu kamin lokacina yayi.

No comments:

Post a Comment