Sunday, 24 December 2017

Bisa umarnin shugaba Buhari: shugaban kamfanin mai na kasa, Maikanti Baru ya fara rangadi a gidajan mai dan shaida abinda ke faruwa game da wahalar man da ake ciki

hoton shugaban kamfanin mai na NNPC da tawagarshi daga shafin hutudole.com
Bisa umarrnin shugaban kasa, Shugaban rukunin kamfanin man fetur na najeriya, NNPC a takaice, Maikanti Baru da tawagarshi, sun fara zagayawa gidajen mai domin ganin irin yanda abubhwa ke gudana dangane da wahalar man da ake ciki a kasarnan.hoton shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga shafin hutudole.com
Dazune shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fitar da sanarwa akan matsalar wahalar man fetur da ake dama da ita inda yace abin takaicine kuma yana tausayawa 'yan Najeriya bisa irin yanda suke wahalar bin layukan shan maidain, ya kara dacewa ana sanar dashi abubuwan dake gudana akai-akai.

Kuma hukumar Kamfanin mai na NNPC sun bashi tabbacin cewa akwai mai da aka shigo dashi kasarnan akuma an fara rarrabashi, nan da 'yan wasu kwanaki kadan za'a fita daga wannan wahalar man.

No comments:

Post a Comment