Sunday, 24 December 2017

Buhari Ya Ki Amincewa Da Bukatar Dillalan Mai Na Kara Kudin Fetur

Shugaba Muhammad Buhari ya ki amincewa da bukatar kungiyar dillalan mai wadanda suka nemi gwamnati ta yi karin farashin man fetur don ganin sun rage asarar da suke yi kamar yadda suka yi ikirari.


Tuni dai, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustafa ya jaddada cewa dillalan man ne suka janyo wannan karancin fetur da gangan inda ya tabbatar da cewa kwanaki biyu bayan bukukuwan Kirismeti, fetur zai wadata a duk fadin kasar nan.
Rariya

No comments:

Post a Comment