Saturday, 9 December 2017

Cristiano Ronaldo da mahaifiyarshi tare da 'yan uwanshi suna tayashi murnar lashe kyautar Ballon d'or

Tauraron dan kwallon Duniya, Cristiano Ronaldo kenan, da shekaran jiya ya lashe kyautar gwarzon dan kwallo ta ballon d'or karo na biyar, anan Ronaldo dinne da mahaifiyarshi, rike da kyautar da ya lashe ta Ballon d'or.Allah sarki, soyayyar uwa da da dabance, a wata hira da aka taba yi da ita kwanaki, mahaifiyar Ronaldon tace, lokacin tana dauke da cikinshi taso ta zubar dashi, amma Allah yasa hakan be faru ba.

Ta kara da cewa wani lokacin Ronaldon yakan tsokaneta yace mata, kingani da bakiso ki haifeniba amma gashinan nine ke taimakon duka gidan, sai su fashe da dariya, kamar yanda tace.


Anan Cristianonne da 'yan uwanshi su uku, daya namiji biyu mata, rike da kyautar tashi.

No comments:

Post a Comment