Thursday, 7 December 2017

Cristiano Ronaldone ya lashe kyautar Ballon d'or ta wannan shekarar: ya kamo Messi

TAuraron dan kwallon kafa, dan kasar Portugal me bugawa kungiyar Real Madrid, Cristiano Ronaldo ne ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon ta shekara ta Ballon d'or 2017, hukumar dake shirya wannan gasar ta kasar Faransa ce ta bayyana sunan dan wasan a matsayin wanda yayi zarra, ya doke abokan karawarshi Messi daga Barcelona da kuma Neymar daga PSG.




Tun a farko dai mutane talatinne aka ware da ake tunanin zasu iya lashe wannan gasa, akayi tankade da rairaya, suka dawo mutum uku, yau gashi Cristiano ne yayi nasara.

Wannan dai shine karo na biyar da dan wasan yake lashe wannan kyauta, hakan yasa sunzo kan-kan-kan da abokin hamayyarshi, watau Messi.

No comments:

Post a Comment