Saturday, 30 December 2017

Dambarwar data faru da baza'a manta da itaba a masana'antar fina-finan Hausa a wannan shekarar

Yayin da muke bankwana da shekarar 2017 muna kara duba yanda abubuwa suka dauki hankulan mutane, musamman a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood. Anan mun hado wasu batutuwan da suka jawo cece-kuce a masana'antar ta fina-finan Hausa.Batun farko da baza'a manta dashiba wanda ya taso daga masana'antar fina-finan Hausa itace badakalar Umma Shehu wadda abokin aikinta, Aminu Sharif Momo yayi hira da ita a tashar Arewa24.

A cikin wani bidiyo daya watsu kamar wutar daji, momo ya tambayi Umma, wacece ta shayar da Annabi Muhammad (S.A.W), Umma sai tace mishi ya zakamin haka, ya zamu zo nan kuma?. Wannan batu ya dauki hankulan mutane kaita cece kuce da bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.

Sai kuma batun Hadiza Gabon, inda wani ya bata shawarar tayi aure a dandalinta na sada zumunta da muhawara amma sai ta mayar mishi da amsar cewa, ya je ya gayawa babanshi ya saki mamanshi sai ta auri baban nashi. Shima dai wannan batu ya matukar dauki hankulan mutane sosai inda da dama suka baiwa Hadizar laifi.

Sai kuma batun fada tsakanin Ali Nuhu da Rahama Sadau, shima wannan batun ya taso inda aka rika yayata cewa Ali Nuhun ya shirya wani fim ya gayyanci Nafisa Abdullahi wadda ake yada cewa basa ga maciji da Rahama Sadau, shine sai Rahamar taji haushi harta fadiwa Alin wasu kalaman da basu dace ba. Babu dai wanda ya bayyana shedar zahiri wadda ta tabbatar da cewa hakan ta faru, amma a tsakanin wasu masoyan jaruman guda biyu, anyi ta kalaman batanci da zage-zage.

Daga karshedai komi ya lafa, domin Ali da Rahama sun hadu suna Raha, wanda hakan yake nuna babu abinda ya faru ko kuma sunyi sulhu.

Sai kuma batun Sa'adiya Adam, wadda ta fitar da wani gajeren bidiyo tana tallar wani fim wanda za'a nuna a Ado Bayero Mall, Sa'adiya tayi subutar baki a cikin bidiyon inda tace Ado bayero Malt, wannan batu shima ya dauki hankulan mutane sosai. Amma daga baya Sa'adiya ta fito ta gyara kuskurenta kuma ta nemi a rika musu uzuri idan sunyi kuskure.


Sai kuma batun Adam A. Zango, Adamu yayi abubuwa da dama da suka dauki hankulan mutane a wannan shekarar. Na farko shine batun gyara da yayi ikirarin zai kawo a masana'antar fina-finan Hausa, inda yace wasu tsiraru daga cikinsu suna jawo musu zagi, saboda haka bazai tsaya yana kallo a batamishi da iyalanshi sunaba, Adon yace, a cikin wata sanarwa daya fitar, ana tsula tsiya kala-kala a masana'antar tasu kuma a shirye yake ya kawo gyara.

Haka kuma a wani zuwa da yayi kasar Kamaru, Adam A. Zango yace mutanen da suka taru don kallonshi, sunkai kimanin Dubu goma, yawan mutanen da wani dan wasa ko mawaki be taba tarawa ba. Wannan batun shima ya dauki hankulan mutane

Hakanan Adamu ya gayawa masu cinshi gyara idan yayi magana da turanci ko kuma yayi rubutu da turancin akan cewa su daina,dan shi baice ya iya turanciba, suje gurin wadanda sukace sun iya su rika musu gyara, wannan batun shima ya yadu sosai.

Sai kuma batun yafewa Rahama Sadau laifin da tayi na rungumar mawaki Classiq, Rahamar tayi takakkiya har garin kano, ta rubuta wasikar neman afuwa, Ali Nuhu ya mata jagora taje ta kaiwa hukumar fim din ta Kano, Haka kuma ta shiga gidan rediyo inda nan ma ta bayar da hakuri ga duk wanda abinda tayi be mashi dadiba, amma har yanzu hukumar fim ta kano bata bayyana cewa ta yafe mataba.

Sai kuma batun Rahama Sadau din dai har ila yau, Yau, Asabar, Sati guda daidai kenan da Jarumar ta bayar da dama ga masoyanta a dandalinta na Instagram cewa su mata duk tambayar da suke so zata basu amsa,  a cikin wadanda suka mata tambaya, an samu mutum biyu da suka tambayeta shin budurcinta yana nan ko ta rasashi?, Rahamar ta fadi cewa "Na rasa budurcina", labarin da shafinann na hutudole.com ne ya fara bugashi kuma ya watsu kamar wutar daji, shima ya jawo cece-kuce sosai a tsakanin al'umma.

Wasu kenan daga cikin batutuwan da suka dauki hankula a masana'antar fina-finan Hausa a wannan shekarar da muke bankwana da ita.

No comments:

Post a Comment