Friday, 22 December 2017

Daya daga cikin matasan da Kwankwaso ya dauki nauyin karatunsu zuwa kasar Jordan: Fatima Gwadabe Abba ta zama Mace ta farko data iya tukin jirgin sama daga jihar Kano

Wannan baiwar Allahn me suna Fatima Gwadabe Abba na daya daga cikin matasa dari da tsohon gwamnan jihar Kano, lokacin yana gwamna, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya dauki nauyin karatunsu zuwa kasar Jordan inda suka koyi tukin jirgin sama, yanzu Fatima ta gware da tukin jirgi, ta yanda zata iya tukashi ita kadai ba tare da me koyamataba.


Hakan yasa Fatima ta zama mace ta farko daga jihar Kano data iya tukin jirgi.

Muna tayata murna da fatan Allah ya tsare, ya kuma karo mana irinta.

No comments:

Post a Comment