Saturday, 30 December 2017

Fadar shugaban kasa tayi bayanin yanda aka samu sunan matattu a cikin wadanda shugaban kasa ya baiwa mukamai

Bayan sunayen wadanda shugaba Buhari ya baiwa mukami sun bayyana ta hannun sakataren gwamnatin tarayya, an samu sunayen kusan mutum uku  da suka mutu a cikin sunayen.Wannan ya jawo cece-kuce tsakanin 'yan Najeriya, abin ya baiwa mutane da yawa mamaki, saidai mai magana da ywun shugaban kasar, Garba Shehu ya fito yayi bayanin yanda abin ya kasance.

Yace an hada sunayen mutanen da za'a baiwa mukaman tun lokacin tsohon sakataren gwamnatin tarayyar, Babachir Lawal, a shekarar 2015, amma gwamnoni suka ki amincewa da sunayen, wannan yasa aka nada wani kwamiti wanda ciki hadda gwamnonin, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya shugabanceshi, aka sake duba sunayen a shekarar 2016.

Amma sakataren gwamnatin yace za'a sake duba sunauen a mayeau da wadanda suka cancanta.

No comments:

Post a Comment