Tuesday, 19 December 2017

Gwamnonin Najeriya sunyi taron gaggawa da shuwagabannin majalisun tarayya a Abuja akan kudin da za'a ware dan yaki da Boko Haram

Da yammacin yau talatane gwamnonin Najeriya sukayi wani taron gaggawa a Abuja da shugabannin majalisun tarayya, shugaban kungiyar gwamnonin, gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari  ya bayyana cewa sun zauna tsakaninsu sun amince da maganar cire dala biliyan daya daga asusun rara man fetur dan a saiwa sojoji kayan aikin da zasu yaki kungiyar boko Haram da kuma kula dasu yanda ya kamata.Gwamna yari yace hakan nada muhimmanci dan maganar tsaro ba abubane da za'a siyasantar dashi ba, haka kuma dangane da masu ganin cewa hakan bai daceba ko kuma kudin sunyi yawa, ya bayyana cewa a lokacin tsohon shugaban kasa Jonathan dala biliyan biyu aka fitar daga asusun rar da akayi amfani dasu wajan yakin Boko Haram.

Hakama Lokacin tsohon shugaban kasa 'yar Aduwa shima dala biliyan biyar aka fitar dan aiki a Nija Delta, saboda haka wannan abune da bai kamata a siyasantar dashiba, ba sabon abubane kuma dan cigaban kasarnanne.

No comments:

Post a Comment