Tuesday, 12 December 2017

Hoton Atiku durkushe a gaban IBB ya dauki hankulan mutane

A makon daya gabatane tsohon mataimakin shugaban kasa, wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, wanda shima kusane a jam'iyyar PDPn, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ziyara a gidanshi dake jihar Naija.Wannan hoton daya nuna tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar dukushe gaban tsohon shugaban kasa, IBB, ya dauki hankulan mutane, musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

Wasu dai sunce girmamawace tasa Atikun yayi haka, wasu kuwa sunce a'a yana neman tsohon shugaban kasar ya goyamai bayane a burinshi na fitowa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu, shine dalilin dur kusawar tashi a gaban IBB.

Amma koma menene, shidai be bayyana hakan ba da kanshi

No comments:

Post a Comment