Friday, 8 December 2017

Hotunan kamin biki masu tsafta da suka sha yabo

A wannan zamani da ake daukar hotunan kamin aure wanda ake nunawa 'yan uwa da abokan arziki, kai harma da Duniya baki daya, da mafi yawanci zakaga ana rungume-rungume da wasu abubuwa da basu dace ba, wani lokacinma zakaga amaryar ta saka kaya masu nuna tsiraici duk da sunan wai hoton kamin biki, sai ga wani Ango, soja da Amaryarshi sun dauki hoton kamin biki me tsafta daya dauki hankulan mutane aketa yabonsu.Hotunan nasu sun matukar birge, babu rungume-rungume, babu kama hannu kuma matar ta saka kayan mutunci, hatta gashin kanta ta rufeshi da kyau, wannan abu yayi.
Muna musu fatan Alheri da kuma Allah yasa ayi lafiya ya sanya Alheri a cikin wannan aure.


No comments:

Post a Comment