Tuesday, 26 December 2017

Hukumar kula da sayar da man fetur sun rabawa jama'a man fetur din wani gidan sayar da man kyauta

Runduna ta musamman akan magance matsalar karancin man fetur da ake fama da ita, karkashin jagorancin shugaban rukunin kamfanin mai na kasa, NNPC, Maikanti Baru, sun gano wani gidan mai dake sayar da litar mai sama da naira dari biyu a babban birnin tarayya, Abuja.Kuma gidan man bashi da lasisin sayar da man, dalilin haka aka aka rabarwa da mutane man kyauta, wanda yawanshi yakai lita dubu sha shida.

No comments:

Post a Comment