Tuesday, 26 December 2017

Hukumar NNPC takai samame gurin wasu 'yan Bumburutu inda tayi babban kamu

A yammacin jiya, Litininne shugaban rukunin kamfanin mai na kasa, NNPC a takaice, Maikanti Baru tare da tawagar jami'an tsaro suka kai samame wani yankin babban birnin tarayya Abuja inda suka bankado wasu dubunnan litocin mai da aka boye, 'yan bumburutu suke sayarwa a tsadajjen farashi.An dai kama 'yan bumburutun da kuma man da aka tarar a gurin.

Dama dai hukumar ta NNPC tunda aka fara wannan wahalar man tasha fadin cewa, suna kokarin kawo karshen matsalar amma wasu na nan suna boye man, abinda ke kara tsawwala wahalrman kenan.


No comments:

Post a Comment