Saturday, 30 December 2017

"Idan na dena kwallo shirin fim zan koma yi">>Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo, fitattacen dan wasan kwallon kafa na kungiyar Real Madrid, ya bayyana ra'ayinsa na fadawa harkar shirin fim idan ya daina buga tamola. Shahararren dan wasan da ya lashe kyaututtuka bila adadin a sakamakon kwarewarsa da yin fice a fagen taka leda, yayi tsokacin komawa shirin fim din ne a yayin da manema labarai suka tuntube shi akan komawa fagen siyasa.


Manema labari sun yi wannan tuntuba ne bayan da tsohon dan wasa George Weah, ya lashe zaben shugaban kasar sa ta Liberia a zaben da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata.

Dan wasan na kasar Portugal mai shekaru 32 ya bayyana cewa zai shiga fagen shirin fim kamar yadda wasu tsaffin 'yan kwallo suka yi da suka hadar da; Vinnie Jones, Eric Cantona da kuma David Becham.

A wata ganawa da kamfanin labarai na Sky Italia, Ronaldo ya bayyanawa tsohon dan wasan Juventus, Alessandro Del Piero cewa, ba shi da ra'ayin ajiye kwallo yanzu amma idan hakan ta kasance zai jarraba shirin fim, sa'annan zai ci gaba da kulawa da harkokin kasuwancinsa na kamafanoni, Otel da kuma kwantiragin dake tsakaninsa da kamfanin Nike.
hausa.naija.ng

No comments:

Post a Comment