Monday, 4 December 2017

Jiya kunga Super Moon kuwa, yanda wata ya kara girma sosai gari yayi haske?

Jiyane aka kawo karshen abinnan da ake kira da Super Moon, wani yanayine da ake ganin wata yayi girma sosai ya matso kusa da Duniya, Masu binciken sararin samaniya sun bayyana cewa za'a yishi jiya, watau ranar 3 ga watannan na Disamba.

Mutane da dama har a nan Najeriya sun bayyana ganin Super Moon a jiya, wasuma sunce tun shekaran jiya sunga watan yayi girma sosai kuma gari yayi haske.

Wasu kuma suna harkokin gabansu, basuma san me ya faruba.

Wadannan hotunane daga wasu kasashe daban-daban da Super Moon ya faru a Daren jiya.
Kasashen sun hada da Amurka, Myanmar, Isra'il, fakistan dadai sauransu.The Guardian.

No comments:

Post a Comment