Sunday, 3 December 2017

Kali yanda mutane kimanin dubu goma suka taru dan kallon Adam A. Zango a kasar Kamaru

A cikin satin daya gabatane muka samu labarin cewa tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango ya tafi kasar Kamaru dan yin wasa acan, a wannan bidiyon Adamunne lokacin da ya karasa gurin da zai nishadantar da mutanen kasar ta Kamaru, irin yawan mutanen da suka taru don kallonshi, shi kanshi sun bashi mamaki.
A kiyasi, mutanen sukai kimanin mutum dubu goma, kuma a cikin bidiyon za'a iya jin wasu na kiran sunanshi.

Muna taya Adamu murna da fatan Allah ya dawo dashi gida lafiya.

No comments:

Post a Comment