Tuesday, 19 December 2017

Kalli abinda wani dan majalisa ya gani, tsakar dare a kasar Jordan da ya bashi mamaki

Dan majalisar Jihar Katsina Abdullahi I. Mahuta ya bayyana wani abu daya gani a kasar Jordan daya birgeshi kuma yayi fatan cewa inama wataran a samu irin wannan sanin ya kamatar da cigaba a Najeriya. Wajan karfe biyu da rabi na dare ya leka tagar dakinshi, sai yaga wadannan motocin biyu dake hotonnan na sama, akan titi, gashi wutar kantitin ta tsayar dasu kuma sun tsaya, babu wani jami'in tsaron dake gurin.Abdullahi yace da yaga haka sai ya tuna Najeriya, ya kuma tambayi kanshi, ko yaushe zamu kai irin wannan matsayi na sanin ya kamata da kiyaye doka?.

No comments:

Post a Comment