Thursday, 28 December 2017

Kalli mashin din karya da aka rika alakanta hadarin dan shugaban kasa, Yusuf Buhari dashi

Wannan wani mashinne da aka rika hadashi da labarin cewa wai da shine dan shugaban kasa, Yusuf Buhari yayi hadari, sai dai wannan mashin, kamar yanda rahotanni suka nuna, bama a Najeriya bane, a can wata kasane hadarin ya faru, kuma ya dade da faruwa.Bayan da wani bawan Allah ya lura da wannan labarin karya, ya jawo hankulan mutane akai, da suyi watsi dashi, shima me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin sabbin kafafen watsa labarai, Bashir Ahmad yayi kira da ayi watsi da wannan labari domin bashi da tushe ballantana makama.


No comments:

Post a Comment