Thursday, 28 December 2017

Kalli Nomisgee da wadda zai aura, Fatima

Tauraron me gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arewa24 kuma sanannen mawakin Gambara, Aminu Abba Umar wanda akafi sani da Nomisgee kenan a wannan hoton tare da amaryarshi Fatima.An yi shagali daren jiya inda 'yan uwa da abokan arziki suka taru aka taya Aminu da amaryarshi Fatima Murna, mawaka sun baje kolinsu a gurin inda wasu suka shiryawa Nomisgee din wakar aure ta musamman.


Adam A Zango na daga cikin wadanda suka halarci gurin kuma suka nishadantar da mutane.

Gobe Juma'a idan Allah ya kaimu za'a daura Auren, muna fatan Allah yasa ayi lafita ya kuma bada zuri'a dayyiba.


No comments:

Post a Comment