Sunday, 10 December 2017

Kalli takalmin sama da naira miliyan daya da Atiku ya saka zuwa gurin taron PDP jiya

A jiyane jam'iyyar adawa ta PDP tayi taronta na kasa inda ta zabi sabbin shuwagabanninta, tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya halarci gurin taron kuma takalmin daya saka ya dauki hankulan mutane dan kuwa wani kiyasi ya nuna cewa kudin takalmin sunkai sama da naira miliyan daya.
Takalmin dai ana sayar dashi akan kudi Yuro dubu biyu da dari uku da tamanin da hudu kamar yanda yake a shafin sayar da kayan kawa  na vestiairecollective.com, wanda kudin a nairar Najeriya sun kai kwatankwacin sama da naira miliyan daya.
To ai dama masu iya magana sunce, kuturu da kudinshi, alkaki sai na kasan kwano.

No comments:

Post a Comment