Friday, 29 December 2017

Ko Rahama Sadau zata fara yin fim a kasar Turkiyyane?: Ta hadu da wani me shirya fim na kasar

Korarriyar, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau wadda yanzu haka tana can kasar Cyprus, ta bayyana cewa ta hadu da wani me shirya fina-finan kasar Turkiyya a karin farko, Rahamar ce nan da mutumin a wannan hoton na sama, jarumar wadda dama ta bayyana cewa tana koyon yaren kasar Turkiyyar, da alama, watakila ta fara yin shirin fim acan.Likafar Rahama Sadau dai nata kara cigaba tun bayan korar da aka mata daga masana'antar fina-finan Hausa sanadiyyar rungumar mawaki Classiq da tayi a wani bidiyon waka da suka fito tare.
A nan Rahamarce a wani shagon sayar da kaya na kasar Cyprus din.
Muna mata fatan Alheri.

No comments:

Post a Comment