Saturday, 30 December 2017

Kotu ta daure wani dan damfara shekaru 13,275 a gidan yari

Wata kotun Thailand ta yanke wa wani dan damfara hukuncin daurin sama da shekara 13,000 a gidan yari. Pudit Kittithradilok mai shekara 34 ya yarda cewa ya zambaci mutane ta hanyar shirya wata badakkala inda yayi wa masu zuba jari alkawuran bogi.
Masu shigar da kara sun shaida wa kotun cewa mutumin ya shirya wani taron karawa juna sani.


Ya karfafawa wadanda suka halarci taron kwarin gwiwa da cewa harkar kasuwanci na da alaka da kyau, da yin amfani da motoci da fitar da su.

Kusan mutum 40,000 suka zuba sama da dala miliyan 160 a kamfanoninsa.
An tsare Pudit a gidan yarin Bangkok Remand tun bayan da aka kama shi a watan Agusta, kuma a lokacin an hana bada belinsa.

Kotun ta ci tarar kamfanoninsa biyu wadanda ya yi dai-dai da dala miliyan 20 ga kowanne.
An kuma umarci Pudit da kamfanonin da su biya kimanin dala miliyan 17 ga mutane 2,653 da aka gano na wanda abun ya rutsa da su, da kuma kashi 7.5 cikin dari na ribar shekara zuwa shekara.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment