Monday, 4 December 2017

"Kowa tashi ta fishsheshi">>inji Atiku, bayan da wani ya tambayeshi cewa baya ganin lokaci yayi daya kamata a baiwa matasa damar yin mulki?

 A jiyane tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya sanar da komawarshi tsohuwar jam'iyyarshi ta PDP bayan ya fice daga jam'iyya me mulki, APC, wani me suna Tayo da yaga wannan labari, sai ya tambayi Atikun"Shin wai, baka ganin cewa Najeriya na bukatar sabon shugaba, matashi, me jini a jika, maimakon aita maimaita shuwagabannin da suka taba yi a baya".

Tayo ya kara da cewa" (Atiku) ka tabayin mataimakin shugaban kasa kuma kayi iya kokarinka. Shin bazamu iya baiwa sabbin jini damar zama shuwagabanniba?".
 Atiku ya baiwa Tayo amsa da cewa, "shifa shugabanci,daka ganshi, kamar kasuwancine. Zan kuranta abinda nike sayarwa, in gayawa Duniya cewa yafi kowanne, saboda har zuciyata nasan haka yake, kaima zaka kuranta naka.

A karshe, zamu bar masu saye su zabi wanda zasu siya.

No comments:

Post a Comment