Sunday, 17 December 2017

"Kullun da safe sai baba ya rakamu kofar shiga motar da za'a daukemu zuwa makaranta">>Inji diyar shugaban kasa, Zahara Buhari

Diyar shugaban kasa, Zahara Buhari tabi sahun sauran 'yan Najeriya da suke ta taya mahaifinta murnar zagayowar ranar haihuwarshi, Zaharar ta bayyana cewa mahaifinnasu ya musu tarbiyyar iya magana inda ya tabbatar cewa sun amfani da kalaman da suka kamata a lokacin da suke tasowa.




A sakon data fitar ta dandalinta na sada zumunta da muhawara, Zahara ta bayyana cewa:

"Ina tayaka murnar zagayowar ranar haihuwarka baba, na gode da taimakamin da kayi da ayyukan gida, na gode da rakiyar da kake mana zuwa kofar mota kullun safiya dan daukarmu zuwa makaranta, na gode da kayi kokarin ganin mun rika fadin kalaman da suka kamata, Yanzu nike kara sanin muhimmancin irin wadan can abubuwan daka yimana. Allah yayi Albarka.

No comments:

Post a Comment