Tuesday, 5 December 2017

Kwankwaso yayi alkawarin daukar nauyin karatun dalibai 37 da lokacin yana gwamna ya turasu karatu kasar Misra/Egypt, yanzu kuma gwamnatin jihar ta daina biya musu kudin makaranta

A jiya Litininne tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci kasar Misra/ Egypt inda dalibai talatin da bakwai daya tura koyon ayyukan kiwon lafiya daban-daban lokacin yana gwamnan jihar Kano suka shiga cikin mawuyacin hali, bayanda gwamnatin Kano ta yanzu, Karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta daina biyan kudin makarantar nasu.


Kwankwason ya zauna da hukumar  makarantar sannan sun tattauna inda yayi alkawarin daukar nauyin gaba dayan daliban su talatin da bwakai da kudin aljihunshi har su kammala karatun nasu..

A hotin sama Kwankwasonne ya dauki hoto da daliban.

No comments:

Post a Comment