Saturday, 9 December 2017

"Lallai ka kama iska">>Wani ya gayawa Abba El-Mustafa bayan da aka ganshi a gurin taron PDP

 A yaune jam'iyyar adawa ta PDP tayi babban taronta inda ta zabi sabbin shuwagabannin da zasu jagoranci jam'iyyar tasu, Tauraron fina-finan Hausa, Abba El-Mustafa ya halarci gurin taron, inda har ya dauki hoton kanshi a lokacin da ake taron ya saka a dandalinshi na sada zumunta da muhawara.
Bayan saka hoton na El-Mustafa, wasu masoyanshi sun mai fatan Alheri.

Wani kuwa cewa yayi , "Lalle ka kama iska elmustafa".

No comments:

Post a Comment