Monday, 18 December 2017

Masu aikin titi sun manne motar wani mutum da siminti bayan da yaki cireta daga bakin hanya

Brazil
Wani me harkar sayar da motoci a kasar Brazil yaki yarda ya dauke daya daga cikin motocin da yake sayarwa a lokacin da masu gyaran hanya sukazo aiki. An bukaceshi ya matsar da motar tashi dan ayi aiki amma yace sam baisan da wannan zancemba, ya kara da cewa shekaru ashirin kenan yana harkar mota a bakin hanyar, kawai yau rana tsaka azo a wani cemai ya cireta, to bazai matsarba.


Su kuwa ma'aikatan titin da sukai iya yinsu ya kiya sai kawai suka cigaba da aiki suka zuba sumunti suka manne motar a bakin titin kamar yanda ake iya gani a wannan hoton.

Hukumomin kula da tafiye-tafiye na kasar ta Brazil, bayan da suka samu labarin mutumin sun aiko da mota ta musamman da zata dauke motar tashi amma suka iske har ma'aikatan dake aikin titin sun manneta da sumunti.

Abin ya ba mutane mamaki yayinda wasu kuwa dariya abin ya basu.
thefactspeaks.

No comments:

Post a Comment