Thursday, 14 December 2017

Matashi A Jihar Gombe Ya Dauki Nauyin Karatun Yara Marayu Da 'Ya'yan Talakawa Guda 150 Dake Makarantun Firamare

Wani matashi a jihar Gombe mai suna Kwamred Mustapha Usman Hassan ya dauki nauyin karatun yara marayu da 'ya'yan talakawa sama da 150 dake makarantun firamare. Yaran wadanda suka fito daga anguwanni guda biyar dake yankin Gombe Ta Kudu wadanda suka hada da Bolarin Gabar, Bolari Yamma, Kumbiya-Kumbiya, Pantami da Jekadafari, matashin ya kuma saya musu littattafai da jakunkuna.

Tuni dai jama'ar yankunan suka soma kira ga matashin da ya shigo harkar siyasa don ganin an dama da shi kasancewar zai iya zama wakili nagari, duba da irin ayyukan alkairi da ya saba yi a yankunan nasa.
Daga rariya.

No comments:

Post a Comment