Friday, 15 December 2017

"Me ya bata miki fuska haka?">>Rahama Sadau ta tambayi 'yar uwarta bayan taga wannan hoton nata

Wadannan 'yan uwan korarriyar, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau kenan, masu suna Fatima da A'isha Sadau, sun saka wadannan hotunan nasu a dandalinsu na sada zumunta da muhawara, kuma sun kayatar.Rahama ta tambayi A'ishar me ya bata miki fuska haka?, ta bata amsa da cewa kurajene, hakan ya dauki hankulan mutane yayain da har wasu suka fara gayawa A'ishar irin maganin da zatayi amfani dashi wajan maganin wadannan kuraje da suka bata mata fuska.
Rahamar dai tana can kasar Cyprus inda take wani karatu wanda bata bayyana ko me take karantaba, Mujallar Fim tace ta samu labarin cewa Rahamar zatayi watanni uku a kasar kafin ta dawo gida Najeriya.No comments:

Post a Comment