Monday, 11 December 2017

"Me yasa wai masu kudi basa auren kowa, sai mai kudi dan uwansu?, Nasan yanzu ciki ya shiga">>Wani ya tambayi Zahara Buhari bayan ta saka wannan hoton

Bayan da diyar shugaban kasa, Zahara Buhari ta saka wannan hoton na 'yar uwar mijinta, Maryam Indimi da Angonta Mustafa tana musu addu'ar fatan Alheri, sai aka samu wani yayi mata tambayar data fauki hankulan mutane.

Tambayar da wannan mutumin ya yiwa Zahara itace, "Wai me yasa masu kudi ke auren masu kudi?, ke kuma zahara, na san yanzu ciki ya shiga".

Zuwa yanzu dai Zaharar bata bashi amsaba.

Bayan da wannan bawan Allah yayi wannan tambaya ta dauki hankulan mutane, wasu na ganin tambayar tashi bata dace ba, wasu kuwa sunce yayi tambaya me ma'ana.


No comments:

Post a Comment