Saturday, 23 December 2017

Motar gwamnan jihar Filato ta tsaya shan mai gurin 'yan bumburutu

Ana murna bako ya tafi, ashe yana bayan gari, shekarar data gabata ba'a samu wahalar mai irin wadda aka saba fuskanta duk karshen shekara ba a Najeriya, Kwatsam sai gata a wannan shekarar ta dawo, jama'a da dama sun shiga halin kaka nikayi.


Layin ababen hawa dake jerawa dan shan mai a gidajen mai na kasarnan sun dawo, abin dai babu dadi, 'yan bumburutu sai cin karensu suke babu babbaka, to she har hukumomin gwamnatin abin be bariba, a wannan hoton na sama, motar gwamnan jihar Flatoce, Simon Lalong take shan mai a gurin 'yan bumburutu.

Wannan ya dauki hankulan mutane sosai kuma wasu suka rika fadin anya abinnan zaizo karshe nan kusa kuwa?

Allah shi kyauta ya kawo mana karshen wahalhalun da ake ciki

No comments:

Post a Comment