Friday, 22 December 2017

MU GUDU TARE MU TSIRA TARE>>Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Kayi Ibada akan sharudai guda biyu:
1. Yinta da Ikhlasi.
2. Ynita akan Sunnah.

*Ka nemi yarda guda biyu
1. Yardar Allah.
2. Yardar Iyaye.

*Ka roqi abubuwa guda biyu
1. Samun Rahamar Allah.
2. Tsira daga Azabar Allah.

*Ka kare abubuwa guda biyu.
1. Addinin ka.
2. Mutuncin ka.

*Ka yaqi abubuwa guda biyu:
1. Jahilci.
2. Talauci.


*Kaci moriyar abubuwa guda biyu:
1. Lokaci.
2. Lafiya.

*Ka yawaita tunanin abubuwa guda biyu:
1. Kwanciyar Kabari.
2. Tashin Alkiyama.

*Ka tabbatu akan abubuwa guda biyu:
1. Fadar gaskiya.
2. Rukon Amana.

*Ka rage abubuwa guda biyu:
1. Yawan cin abinci.
2. Yawan bacci.

*Ka yarda da abubuwa guda biyu:
1. Qaddara mai kyau.
2. Qaddara mara kyau.

*Ka fifita soyayya guda biyu:
1. Son Allah.
2. Son Manzon Allah.

*Ka siffantu da dabi'u guda biyu:
1. Ganin girman na sama.
2. Tausayawa na kasa.

*Ka nemi tsarin abubuwa guda biyu:
1. Shedanun cikin Aljanu.
2. Shedanun cikin Muatane.

*Ka sadaukar da rayuwar akan abubuwa guda biyu:
1.Neman ilimi.
2. Yin aiki da ilimi.

*Ka shige gaba a wajan abubuwa guda biyu:*
1. Aikin Alkhairi.
2. Kira ga Alkhairi.

*Ina fatan zakuyi abu biyu:*
1. Aiki da abinda saqon ya qunsa.
2. Turawa 'yan uwa domin su amfana

No comments:

Post a Comment