Monday, 25 December 2017

Osinbajo ya cigaba da rangadin gidajen mai dan ganewa idanunshi irin wahalar da mutane kesha

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo tare da karamin ministan mai, Ibe Kachiku yaci gaba da rangadin gidajan mai daya fara jiya a birnin Legas dan ganewa idanunshi irin yanda jama'a suke fama da wahalar sayan man fetur.Osinbajo ya tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa gwamnati na iya bakin kokarinta dan ganin cewa wannan wahalar man tazo karshe cikin 'yan kwanakinnan bada dadewaba.


No comments:

Post a Comment