Tuesday, 26 December 2017

Rahama Sadau 'yar kwalisa; Kalli wani sabon hotonta

Tauraruwar fina-finan Hausa da Turanci, Rahama Sadau kenan a wannan hoton nata daya kayatar, ta saka wata rika ta musamman dake dauke da sunanta a jiki, Rahamar dai tana kasar Cyprus inda ga dukkan alamu karatu takeyi a jami'ar Easter Mediterranean dake kasar.


Kuma a cikin wata dama data bayar ga masoyanta aka mata tambayoyi ta amsa, ta bayyana cewa, watan Janairu idan Allah ya kaimu zata dawo Najeriya.

Dama dai da jimawa mujallar Fim Magazine ta bamu labarin cewa Rahamar ta tafi kasar Cyprus kuma zatayi watanni uku acan din kamin ta dawo.

Muna fatan Allah ya dawo da ita lafiya.

No comments:

Post a Comment