Wednesday, 6 December 2017

Rahama Sadauce tauaruwar jaridar Leadership ta shekara

Jaridar Leadership ta bayyana fitacciyar, korarriyar jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau a matsayin tauraruwarta ta shekara, Jaridar tace ta baiwa Rahama karramawane saboda irin yanda ta taso a cikin mutane masu irin ra'ayin 'yan mazan jiya amma hakan bai hanata jajircewaba wajan ganin ta shallake duk wani shinge da ake dorawa mata, musamman a Arewa ba, dan ganin ta cimma burinta.
Jaridar ta kuma bayar da misali na irin abubuwan da Rahamar tayi ciki hadda shahararren fim dinta na Rarayi, wanda shine shirin fim na farko da Rahamar ta fara shiryawa da kanta kuma a shekarar da ya fito, ya zama zakaran gwajin dafi, ya lashe kyautar fim din da yayi fice ta City Peple Award.

Muna tayata Murna.

No comments:

Post a Comment